The news is by your side.

Kotu ta umarci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta biya Yahaya Bello diyyar naira biliyan 1 kan ɓata suna

60

Wata Babbar Kotu a Lokoja, Jihar Kogi, ta umarci Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta biya tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, diyyar naira biliyan 1 kan kalamai na ɓata suna.

Hukuncin ya fito ne a ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, inda alƙalin kotun, A.S. Ibrahim, ya ce mai ƙarar ya tabbatar da hujjojinsa bisa ƙa’idojin doka.

Shari’ar mai lamba HCL/16/2023 ta shafi kalaman da Akpoti-Uduaghan ta yi ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2022, a shirin “The Morning Show” na tashar Arise TV.

Alƙalin ya yanke cewa kalaman da ta bayyana Bello a matsayin “mai kisan kai, mai aikata miyagun ayyuka, da zama barazana ga al’ummar Jihar Kogi” sun ɓata masa suna kuma ba su da hujja.

A cewar kotun, “hirar da wadda ake ƙara ta yi a ranar 4/11/2022 a shirin Arise TV ta ɓata martabar mai ƙarar kuma ta shafi mutuncinsa.”

Kotun ta kuma haramta wa Akpoti-Uduaghan da wakilanta ko abokan hulɗarta yin irin waɗannan kalamai a nan gaba a gidajen rediyo da talabijin.

Haka kuma, alƙalin ya ce za a biya diyyar naira biliyan 1 ga Yahaya Bello saboda ɓarnar da aka yi masa.

Tun da farko, Bello ne ya shigar da ƙara yana mai cewa kalaman sun ɓata masa suna a idon jama’a.

Lauyan Akpoti-Uduaghan, Johnson Usman, ya ƙalubalanci hurumin kotun yana mai cewa shari’ar cin zarafin tsarin kotu ce, amma lauyan Bello, Friday Ekpa, ya musanta hakan.

A baya, Babbar Kotu ta Kogi ta tabbatar da cewa tana da hurumin sauraron ƙarar, kuma kotun ɗaukaka ƙara ta goyi bayan wannan hukunci bayan ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da aka shigar.