The news is by your side.

Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68.32

55

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaɓa hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 mai darajar naira tiriliyan 68.32 a ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026.

Sanarwar hakan ta fito ne cikin wata takarda da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.

Kasafin kuɗin ya tanadi naira tiriliyan 4.799 don kuɗaɗen da doka ta tanada da kuma naira tiriliyan 15.8 don biyan basussuka.

Haka kuma, an ware naira tiriliyan 15.4 don kuɗaɗen gudanarwa, yayin da aka tanadi naira tiriliyan 32.2 domin ayyukan raya ƙasa.

A cewar sanarwar, kusan kashi 50 cikin ɗari na kasafin kuɗin na ɓangaren zuba jari ne, wanda ke nuna ƙudurin gwamnati na tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi, tsaro da kuma bunƙasa ababen more rayuwa.

Shugaban ya kuma amince da dokar da ta tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren zuba jari na kasafin kuɗin 2025 daga ranar 31 ga Maris, 2026 zuwa 30 ga Yuni, 2026.

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ma’aikatu da hukumomi damar kammala manyan ayyukan raya ƙasa da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar.

Tinubu ya umurci ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati su tabbatar da amfani da kuɗaɗen cikin gaskiya, inganci da kuma a kan lokaci.

Haka kuma ya yaba wa Majalisar Dokoki ta ƙasa bisa yadda ta gaggauta tantancewa da amincewa da kasafin kuɗin.

A cewarsa, haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin ci gaban ƙasa.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a ɗauki wani ɓangare na kasafin kuɗin ta hanyar karɓar bashin waje sama da dala biliyan 21 domin cike giɓin kuɗaɗe.