The news is by your side.

Jigawa Ta Yi Fice Yayinda INEC Ta Yi Rajistar Sabbin Masu Zaɓe Kusan Miliyan 3 da Rabi a Najeriya

61

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa a Najeriya (INEC) ta sanar da cewa ta yi rajistar sabbin masu zaɓe sama da miliyan 3.4 a mataki na biyu na shirin rajistar masu zaɓe da ake yi a faɗin ƙasar.

A cewar rahoton mako na 13 da aka fitar a Abuja, an kammala rajistar mutane 3,441,121 zuwa ranar 3 ga Afrilu, ciki har da waɗanda suka yi rajista ta yanar gizo da kuma waɗanda suka je cibiyoyi kai tsaye.

INEC ta ce mutane 2,068,384 sun yi rajista ta intanet, yayin da 1,372,737 suka yi ta hanyar halartar cibiyoyin rajista.

Rahoton ya nuna cewa jihar Jigawa ce ta fi yawan masu rajista da 201,047, sai Legas da 181,095, yayin da Kano ke matsayi na uku da 177,681.

Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 su ne suka fi yawa, inda suka kai kashi 68.43 cikin ɗari na jimillar masu rajistar.

Haka kuma mata sun fi maza yawan rajista, inda suka kai kashi 55.86.

Ɗalibai ne suka fi yawa a ɓangaren sana’a, inda suka kai sama da miliyan 1.2, sai ƴan kasuwa da manoma da masu kamun kifi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 48,330 masu naƙasa sun yi rajista, tare da jaddada cewa alƙaluman na wucin gadi ne kafin tantancewa ta ƙarshe.

INEC ta buƙaci duk waɗanda suka cancanta amma ba su yi rajista ba da su gaggauta yin hakan kafin wa’adin ya cika.