The news is by your side.

Rikici Ya Kunno Kai a APCn Bauchi Kan Shirin Karɓar Gwamna Bala Zuwa Jam’iyyar

72

Rikici mai tsanani ya kunno kai a cikin jam’iyyar APC a jihar Bauchi sakamakon shirin karɓar Gwamna Bala Mohammed cikin jam’iyyar, kamar yanda HAUSA TIMES ta samo daga PUNCH.

Wannan saɓani ya bayyana ne a wani taron ƴan majalisar jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Shugabannin jam’iyyar sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan yiwuwar sauya sheƙar gwamnan, musamman dangane da tasirin hakan ga tsarin jam’iyyar a jihar.

Domin magance matsalar, an amince da kafa kwamitin ƙoli domin tsara matsaya da kuma tattaunawa da shugabancin jam’iyya na ƙasa.

Muƙaddashin sakataren kwamitin, Dabo Ismail, ya ce kwamitin zai tsara sharuɗɗan da za a bi wajen karɓar gwamnan tare da tabbatar da cewa an haɗa kan duk masu ruwa da tsaki.

Ya bayyana cewa, “Ba a hana gwamnan shiga APC ba, amma dole ne a bi tsarin demokaraɗiyya na cikin gida.”

Shima sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Sama’ila Dahuwa, ya nuna rashin jin daɗi kan yadda aka tafiyar da lamarin ba tare da tuntuɓar ƴan jam’iyyar a jihar ba.

A cewarsa, “Wannan watsi da mu ba abin yarda ba ne,” yana mai gargaɗin cewa irin hakan na iya haddasa rabuwar kai a jam’iyyar.

Rahoton ya ƙara da cewa wannan batu ya samo asali ne daga sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027, inda ake zargin gwamnan na neman sabuwar mafaka bayan ya nuna niyyar barin PDP.

Gwamnan ya taɓa cewa, “Mun yi ƙoƙarin sulhu amma bai yi nasara ba. Har mun duba yiwuwar shiga APC, amma muka ga ba a son mu a can.”

Masu sharhi sun ce, yiwuwar shigar gwamnan na iya ƙarfafa APC a Bauchi, amma kuma zai iya haifar da rikici tsakanin tsofaffin ƴan jam’iyyar.