The news is by your side.

Atiku Ya Ɗauki Kamfanin Kyautata Alaƙa na Amurka Aiki Gabanin Zaɓen 2027

84

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya rattaba hannu kan kwangilar dala miliyan 1.2 da wani kamfanin gyaran alaƙa a Amurka domin ƙarfafa matsayinsa a siyasa, in ji rahoton PREMIUM TIMES.

Takardun da aka shigar a ma’aikatar shari’a ta Amurka sun nuna cewa an ƙulla yarjejeniyar ne ta tsawon watanni 12, inda kamfanin zai taimaka wajen hulɗa da gwamnati da majalisar dokokin Amurka.

An ce, aikin zai haɗa da inganta martabar Atiku da bayyana manufofinsa ga ƙasashen waje.

Haka kuma zai taimaka wajen shirya ganawar Atiku da manyan jami’an Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa, Atiku ya daɗe yana amfani da irin waɗannan kamfanoni domin inganta alaƙarsa da Amurka. Wannan na daga cikin yunkurinsa na sake fafatawa a zaben shugaban kasa.