The news is by your side.

Ƴan Sanda Sun Fara Bincike Kan Ɗan Da Ya Babbake Mahaifinsa Har Lahira a Jigawa,

78

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta fara bincike kan wani lamari mai tayar da hankali inda ake zargin wani matashi ya kashe mahaifinsa ta hanyar ƙona shi da wuta a Kazaure.

Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Afrilu, 2026, da misalin ƙarfe 6:30 na safe, a unguwar Magama.

A cewar sanarwar rundunar, an zuba wani abu mai kama da fetur a jikin mutumin mai shekaru 60 kafin a banka masa wuta.

Daga bisani ƴan sanda sun kama ɗansa, Kabiru Nuhu mai shekaru 27, wanda aka same shi da raunuka da ƙonewa a jikinsa.

An garzaya da wanda aka ƙona asibiti, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

Kwamishinan ƴan sanda, CP Haruna Alaba Yahaya, ya yi Allawadai da lamarin, yana mai cewa za a tabbatar da adalci a binciken.

Ya kuma buƙaci jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu tare da kai rahoton duk wasu rikice-rikice ga hukumomi. Rundunar ta tabbatar da cewa za a miƙa wanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.