The news is by your side.

Sauyin Siyasa a Kebbi: Aminu Bande Ya Fice Daga PDP, Ya Koma ADC

45

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC bayan ya fice daga PDP.

An karɓe shi ne a hukumance a sakatariyar jam’iyyar ADC ta jihar a ranar Litinin, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sufiyanu Bala, ya miƙa masa katin zama mamba.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa da ya aika wa shugaban mazaɓar PDP ta Nasarawa I a Birnin Kebbi, Bande ya bayyana cewa matakin ya fara aiki nan take.

Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani, nazari da tattaunawa da magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ƙara da cewa dalilin sauyin jam’iyyar shi ne don dacewa da ra’ayin al’umma da suke so a samu ingantacciyar tafiyar siyasa mai ɗorewa da gaskiya.

“Mun yanke wannan shawara ne domin cimma manufofin kyakkyawan shugabanci mai adalci da gaskiya a Kebbi da Najeriya baki ɗaya,” in ji shi.

Duk da cewa bai bayyana inda zai dosa ba a wasiƙar murabus ɗin farko, karɓuwarsa a ADC ta tabbatar da sabon matsayinsa a siyasance.

Bande ya sha kaye a hannun gwamnan jihar mai ci, Nasir Idris, a zaɓen 2023.

Masu lura da al’amuran siyasa sun ce wannan sauyin na iya ƙara zafafa fafatawar siyasa a jihar gabanin zaɓen 2027.