The news is by your side.

Rigima Ta Ɓarke a APCn Katsina Kan Takarar Yusuf Buhari, Masu Ruwa da Tsaki Sun Yi Fatali da ‘Ɗauki Ɗora’

64

Saɓani ya ɓarke a jam’iyyar APC a Jihar Katsina bayan wasu masu ruwa da tsaki sun ayyana Yusuf Buhari a matsayin wanda suke so ya tsaya takarar majalisar wakilai.

A cewar rahoton Daily Trust, an yanke wannan hukunci ne a wani taro da aka gudanar a Sandamu.

Sai dai a wani taron na daban, wasu manyan ƴan jam’iyyar daga ƙananan hukumomi biyar sun yi watsi da wannan mataki, suna zargin ana ƙoƙarin ƙaƙabawa jama’a ƴan takara.

Sun ce wasu jami’an gwamnati ne ke yaɗa wannan ra’ayi ba tare da amincewar gwamna ba.

Barrista Usman El-Marzuk ya ce, “babu inda gwamna ya ce a ƙaƙabawa mutane ƴan takara”, yana mai kira da a mutunta tsarin demokaraɗiyya.

Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar Daura ya buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin.

Masu sharhi sun ce wannan rikici na iya janyo rabuwar kai a jam’iyyar idan ba a shawo kansa da wuri ba.