Browsing Category
Tsaro da Shari’a
Laifuka, tilasta doka, da shari’a.
Harin Ƴan Bindiga a Kebbi: Gidaje Sun Ƙone, Mutane Sun Tsere
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai farmaki cikin dare a wasu ƙauyuka a Jihar Kebbi, lamarin da ya jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyi.
Harin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyukan Gebe, Kawara da Kalkami a ƙaramar hukumar Shanga.!-->!-->!-->…
Ban Tsorata Ba – Seun Okinbaloye Ya Maida Martani ga Minista Wike
Ɗan jaridar Channels TV, Seun Okinbaloye, ya bayyana cewa bai tsorata ba duk da kalaman barazana da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi masa.
Ya bayyana hakan ne yayin shirin siyasa na Sunday Politics.
Ya ce, “Ina so in bayyana!-->!-->!-->!-->!-->…
Wani Hari Ya Yi Sanadin Mutane 17 a Benue, Borno Ma Ta Fuskanci Harin Ƴan Ta’adda
Aƙalla mutane 17 ne suka mutu a wani hari da aka kai a yankin Mbalom na ƙaramar hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benue.
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun shiga yankin suna harbe-harbe tare da ƙona gidaje.
Lamarin ya janyo asarar!-->!-->!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Ceto Mutane 31 Cikin Waɗanda Aka Sace Ranar Lahadin Nan a Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto mutane 31 da aka sace yayin ibadar Easter a ƙauyen Ariko da ke Kachia a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne bayan sojoji sun samu kiran gaggawa game da harin.
A wata sanarwa da hedikwatar sojin!-->!-->!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Fara Bincike Kan Ɗan Da Ya Babbake Mahaifinsa Har Lahira a Jigawa,
Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta fara bincike kan wani lamari mai tayar da hankali inda ake zargin wani matashi ya kashe mahaifinsa ta hanyar ƙona shi da wuta a Kazaure.
Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Afrilu, 2026, da misalin ƙarfe!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda Sun Kama Mutane Huɗu Da Zargin Kisan Gilla Wa Wani Kan Saɓani a Katsina
Rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a wani kisan gilla da ya yi sanadin mutuwar wani KC Joe a ƙauyen Kokami.
Kakakin rundunar, Abubakar Sadiq, ya ce ana ci gaba da bincike yayin da ake tsare da!-->!-->!-->…
Atiku Da ADC Sun Yi Allawadai Da Barazanar Da Wike Ya Yi Wa Ɗan Jarida, Sun Nemi Ya Gaggauta Neman…
Jam’iyyar ADC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi kakkausar suka ga kalaman Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda ya yi barazanar harbe ɗan jarida Seun Okinbaloye.
Wannan ya biyo bayan wata muhawara a shirin Politics!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Cafke Masu Sanye da Kakin Bogi, Sun Hallaka Ƴan Ta’adda Uku a Filato
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation ENDURING PEACE sun cafke wasu mutane biyu da ke sanye da kayan jami’an tsaro na bogi tare da kashe ƴan ta’adda uku a wasu samame da suka kai a Jos ta Arewa da kuma ƙaramar hukumar Wase a Jihar!-->…