The news is by your side.

Majalisar Kano ta amince da Garo a matsayin mataimakin gwamna bayan an kasa ƙalubalantarsa

26

Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da naɗin Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna bayan tantance shi.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunansa ga majalisar a ranar 22 ga Afrilu, 2026.

Mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Bello Butubutu, ya shaida wa BBC cewa sun tabbatar Garo ya cika sharuɗɗan doka ciki har da ilimi da shekaru.

Ya ce Garo ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukuma da kwamishina, kuma yana da gogewar jagoranci.

Butubutu ya ce bayan gabatar da rahoton tantancewar, babu wanda ya ƙalubalanci shi a zauren majalisar.

Naɗin na zuwa ne bayan murabus ɗin tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, 2026.

Rahotanni sun danganta murabus ɗin da saɓani tsakanin gwamna da mataimakinsa da wasu masu ruwa da tsaki.

Majalisar ta ce za ta ci gaba da aiki tare da sabuwar gwamnatin domin cigaban jihar.