The news is by your side.

Atiku Abubakar ya ce zaɓen 2027 na iya zama na ƙarshe a takararsa ta shugaban ƙasa

80

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zaɓen shugaban ƙasa na 2027 na iya zama fafatawarsa ta ƙarshe domin shugabancin Najeriya, yana mai danganta hakan da shekarunsa da kuma muhimmancin zaɓen.

Atiku, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise Television a yammacin ranar Laraba.

Da aka tambaye shi ko kusantar cika shekaru 80 a 2027 zai ƙara masa wahalar yin takara, Atiku ya ce hakan na iya zama fitowarsa ta ƙarshe a siyasa ta wannan mataki.

Ya ce, “Tabbas eh, saboda abubuwan da ke kan gado sun fi yawa kuma ina ganin wannan zai kasance fitowa ta ƙarshe.”

Atiku ya yi yunƙurin zama shugaban ƙasa sau da dama tun bayan dawowarsa siyasa a karshen ƙarnin da ya gabata.

A shekarar 1993 ya shiga takarar fidda gwani a jam’iyyar Social Democratic Party kafin ya janye wa marigayi Moshood Abiola.

Daga bisani ya tsaya takara a 2007 a jam’iyyar Action Congress inda ya sha kaye a hannun marigayi Umaru Musa Yar’Adua.

Haka kuma ya sake tsayawa a 2011 a ƙarƙashin Action Congress of Nigeria inda ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan.

Ya koma PDP ya kuma tsaya takara a 2019 inda ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.

A zaɓen 2023 kuma ya kasance ɗan takarar PDP amma ya sha kaye a hannun Bola Tinubu na APC.