Majalisar Zamfara Ta Dakatar da Shugabannin Ƙananan Hukumomi Biyu Kan Zargin Almundahana
Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi biyu bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da kuma ƙin bada bayanai kan yadda aka kashe su.
Waɗanda abin ya shafa sun hada da Mannir Mu’azu Haidara na Kaura Namoda da Umar A. Faru na Bukkuyum.
Kakakin majalisar, Bello Kurya, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Ya bayyana cewa kwamitin kula da ƙananan hukumomi ne ya gabatar da rahotonsa a zaman majalisar ta bakin mataimakin kakakin majalisa, Adamu Aliyu Gumi.
Kurya ya ce, “Kwamitin ya bada shawarar dakatar da shugabannin biyu saboda ƙin amsa gayyata domin su yi bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ba su.”
Bayan tattaunawa ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisa, Bilyaminu Moriki, an amince da dakatar da su nan take har sai an kammala bincike.
An kuma umurce su da su miƙa ragamar mulki ga mataimakansu ba tare da ɓata lokaci ba.
Majalisar ta bayyana rashin mutunta ta da kuma rashin gaskiya a matsayin manyan laifukan da suka janyo wannan mataki.
Kurya ya ƙara da cewa, majalisar na da ƙudurin tabbatar da gaskiya, da kula da dukiyar jama’a, da kuma kare amana da al’umma suka ɗora wa shugabanni.
Ƙoƙarin jin ta bakin shugabannin da aka dakatar bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntuɓarsu ba har lokacin haɗa wannan rahoto.