The news is by your side.

INEC Ta Dakatar da Shirye-Shiryen Sabunta Rijistar Masu Zaɓe Bayan Zarge-Zarge

78

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta umarci dukkan kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) da su dakatar da duk wani shiri da tallatawa game da sabunta rijistar masu zaɓe da aka shirya yi a faɗin ƙasar.

Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Afrilu, 2026, wadda sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta rattaba hannu a kai.

Sai dai hukumar ta buƙaci kwamishinonin da su ci gaba da shirye-shiryen cikin gida kamar samar da ma’aikata da kuma tanadar na’urorin rajista, yayin da ake jiran umarni na gaba.

Sanarwar ta ce, “RECs su dakatar da duk wani shiri na tallatawa da shirye-shiryen sabunta rijistar masu zaɓe har sai an sake bayar da umarni”.

Wannan mataki na zuwa ne bayan zargin da wani jigo a Majalisar Shari’a ta Najeriya, Dakta Bashir Aliyu Umar, ya yi cewa akwai wani shiri na rage tasirin Musulmi ta hanyar sabunta rijistar.

Tun da farko dai INEC ta sanar da fara wannan aiki daga ranar 13 ga Afrilu, 2026, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen 2027.

Haka kuma hukumar ta sauya taron da za ta yi da kwamishinonin zuwa na yanar gizo maimakon haduwa a Abuja da da aka shirya.

INEC ta buƙaci jami’anta da su ci gaba da zama a jihohinsu suna jiran ƙarin bayani, tare da nuna nadama kan duk wata matsala da hakan ka iya haifarwa.