The news is by your side.

Wasu Ƙungiyoyi Sun Buƙaci Goodluck Jonathan Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

74

Wata gamayyar ƙungiyoyi daga jihohi 36 da Abuja ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.

Shugaban ƙungiyar, Tom Ohikere ne ya bayyana hakan a wani gangami da aka yi a Abuja.

Ya ce wannan kira ya biyo bayan watanni shida na tuntuɓa da aka yi a faɗin ƙasar, inda ya ce, “Ƴan Najeriya suna roƙon ka da ka dawo domin ceto ƙasar nan.”

Ya ƙara da cewa, mutane da dama na goyon bayan dawowar Jonathan kan mulki.

Ƙungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin wanda zai iya haɗa kan al’umma da magance rarrabuwar kawuna.

Ta kuma yi alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar idan ya amince.

Sakataren ƙungiyar, Jibril Mustapha, ya danganta kiran da halin da ake ciki na yunwa da rashin tsaro a ƙasar.

Ya ce, “Ba ma iya kwanciya cikin kwanciyar hankali a yankinmu.”

Wani jigo, Amodu Abacha, ya yabawa Jonathan bisa yadda ya amince da shan kaye a 2015, yana mai cewa hakan alama ce ta gaskiya da kishin ƙasa.

Sai dai har zuwa yanzu, Jonathan bai mayar da martani kan wannan kira ba.