The news is by your side.

Janar na Soji da Wasu Sojoji Sun Rasa Rayukansu a Sabbin Hare-Haren Ƴan Ta’adda a Borno

50

Wani babban jami’in sojin Najeriya mai muƙamin Brigediya Janar da wasu sojoji sun rasa rayukansu sakamakon sabbin hare-haren ƴan ta’adda a wasu yankunan Jihar Borno.

Hare-haren sun faru ne a wurare huɗu daban-daban a daren Laraba, inda aka fara kai farmaki a Pulka da Bakin Ruwa na ƙaramar hukumar Gwoza da misalin ƙarfe 10:30 na dare.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta’addan sun ƙwace wani sansanin soji tare da ƙona kayan yaki da dama.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa, an yi asarar wani babban kwamandan runduna a yankin Benesheikh da ke ƙaramar hukumar Kaga.

Majiyar ta ce, “Abin takaici, mun sake rasa wani jarumin soja a yaƙi da ta’addanci… Allah ya jiƙansa ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashi.”

Ta ƙara da cewa wannan lamari na nuna buƙatar ƙara ƙarfafa dabarun leƙen asiri da tsaro domin tallafawa jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu.

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a Arewa maso Gabas, inda ƴan ta’adda ke kai hare-hare akai-akai kan sansanonin sojoji da kan fararen hula.

Masana tsaro sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara zuba jari a ɓangaren tsaro domin daƙile irin waɗannan hare-hare da kare rayuka da dukiyoyi.