The news is by your side.

Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Mai, Al’umma Na Fargabar Ƙarin Tsadar Rayuwa A Najeriya

57

Matatar Dangote ta sanar da ƙarin farashin man fetur zuwa ₦1,275 kan kowace lita da man dizal zuwa ₦1,950, lamarin da ya ƙara jefa al’umma cikin damuwa kan tsadar rayuwa.

Wani jami’in matatar ya tabbatar da ƙarin, yana mai cewa an yi hakan ne bisa yanayin kasuwannin duniya.

Rahotanni daga petroleumprice.ng sun tabbatar da sabbin farashin.

Wannan ƙarin ya zo ne a daidai lokacin da tattalin arziƙin Najeriya ke fuskantar matsin lamba.

Masana sun ce ƙarin farashin dizal na iya shafar sassa kamar na sufuri, noma da masana’antu.

Ƴan kasuwa ƙanana da masu amfani da janareto za su fi fuskantar tasiri kai tsaye.

“Wannan ƙarin zai ƙara hauhawar farashin kayayyaki,” in ji wani masani.

Najeriya na ci gaba da fama da matsalar wutar lantarki, lamarin da ke ƙarawa ƴan ƙasar dogaro da dizal.

An yi fatan cewa, matatar Dangote za ta rage farashin mai, amma har yanzu farashin na bin kasuwar duniya.

Wannan na nuna cewa har yanzu Najeriya ba ta samu cikakkiyar kariya daga tashin farashin ma a duniya ba.

Masana sun yi gargaɗin cewa idan ba a inganta wutar lantarki ba, matsalar za ta ci gaba.