Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Shekaru 10 Kan Taimaka wa Ƴan Ta’adda a Najeriya
Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Auwal Bello hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari bisa laifin taimakawa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar musayar kuɗi.
Wannan hukunci ya biyo bayan laifukan da ya aikata a lokacin rikicin sauya fasalin naira a 2023.
Mai shari’a Binta Nyako ta ce, Bello ya taimaka wajen sauya kuɗaɗen naira 750,000 ga ƴan Boko Haram, tare da biyan harajin naira 20,000 ga ƙungiyar.
Ta bayyana cewa waɗannan laifuka sun saɓa da dokar hana ta’addanci ta 2013.
Bello ya amsa laifinsa a kotu, inda ya roƙi a tausaya masa.
Sai dai kotu ta yanke masa hukuncin da ya haɗa da na gyaran hali da kawar da tsattsauran ra’ayi.
A wata shari’ar ta daban, an yanke wa Hamat Modu hukuncin shekaru 10 bisa laifukan da suka shafi ta’addanci.
Haka kuma Isah Ali, wanda aka kama yana ɗan shekara 18, ya samu hukuncin shekaru 10 bayan an rage masa wasu tuhume-tuhumen.
Kotun ta kuma yanke wa Shehu Bukar hukuncin shekaru 20 bisa taimaka wa Boko Haram ta hanyar sayar musu da dabbobi.
A wani ɓangaren kuma, an yanke wa Abdullahi Ali hukuncin shekaru 20 bisa samar da man fetur ga mayaƙan ISWAP.
Lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, sun gabatar da hujjoji da suka taimaka wajen yanke hukunce-hukuncen.
Kotun ta jaddada cewa za a ci gaba da ɗaukar matakan shari’a kan duk wanda aka samu da hannu a ayyukan ta’addanci.