Peter Obi Ya Caccaki Tinubu Kan Faruwar Sabbin Hare-Hare Bayan Alƙawarin Da Yai Na Tsayawar Matsalar Tsaro
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan yadda hare-haren tashin hankali ke ƙaruwa a ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.
Obi ya tuna da alƙawarin da shugaban ya yi a Jos cewa irin hare-haren ba za su sake faruwa ba.
“Ƙasa da sa’o’i 24 bayan wannan alƙawari, an sake kai wani harin,” in ji shi.
Ya ce hare-haren sun bazu zuwa jihohi da dama ciki har da Nasarawa, Zamfara, Borno, Benue da Kaduna.
“Wannan gazawa ce ta shugabanci, kuma ƴan Najeriya ne ke biyan farashinta da rayuwarsu,” a cewarsa.
Obi ya jaddada cewa babban aikin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma, amma wannan aiki yana fuskantar gazawa a ɓangaren Shugaba Tinubu.
Ya kuma bayyana halin da ake ciki a matsayin “na buƙatar gaggawa a ƙasa.”
A gefe guda, Shugaba Tinubu ya kai ziyara Jos bayan wani hari da ya kashe fiye da mutane 28, inda ya yi alƙawarin cewa ba za a sake irin hakan ba.
Ya kuma sanar da shirin girke na’urorin sa ido na zamani domin inganta tsaro a yankin.
Sai dai wasu sun soki yadda aka gudanar da ziyarar, suna cewa ba a kai ziyara kai tsaye wuraren da abin ya faru ba, yayin da shugaban ya tsaya iya filin jirgin sama a lokacin.