Tsohon sanatan Jigawa ta Tsakiya, Sabo Muhammad Nakudu, tare da wasu manyan ƴan siyasa sun sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar ADC.
Daga cikin waɗanda suka biyo shi akwai Bala Ibrahim Chamo da Zakari Kafin Hausa, da sauran wasu tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Jigawa.
A yayin sanar da sauyin sheƙar, Nakudu ya ce, sun ɗauki wannan mataki ne domin neman wata jam’iyya mai haɗa kan jama’a da inganta demokaraɗiyya.
Ya ƙara da cewa, ADC na da damar magance matsalolin da ke addabar Jihar Jigawa.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027 ƙarƙashin ADC.
Ya ce, “mun ɗauki wannan mataki ne bayan tuntuɓa mai zurfi da magoya baya”.
Masu sharhi sun ce wannan sauyi zai ƙara zafafa siyasa a jihar kafin zaben 2027.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, APC ba ta fitar da martani kan wannan babban lamari ba.