Ƙwararrun likitoci sun bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na yanke gaɓɓai a Najeriya na da alaƙa da cutar sikari (diabetes), lamarin da ke ƙara jefa al’umma cikin haɗari.
A cewar rahoton Punch, masanan sun ce rashin kula da cutar na haifar da raunuka a ƙafa da kamuwa da cututtuka.
Farfesa Andrew Uloazko ya ce, mutane miliyan 12 zuwa 13 ne ke ɗauke da cutar a Najeriya, da dama ba su ma sani ba.
Haka kuma Farfesa Olufemi Fasanmade ya ce, a kusan kowane mako ana yanke ƙafa daya ko biyu a manyan asibitoci sakamakon cutar.
Masana sun bayyana cewa raunukan ƙafa da ke warkewa da wahala na daga cikin manyan dalilan yanke gaɓɓan.
Likita Mike Ogirima ya ce, “yawan faruwar yanke ƙafa saboda sikari ya zarce na wasu raunuka a wasu wurare”.
Sun buƙaci jama’a da su riƙa duba lafiyar jikinsu, musamman masu fama da sikari, tare da neman magani da wuri.
Rahoton ya kuma yi gargaɗi kan neman magani wajen waɗanda ba kwararru ba, wanda ke ƙara tsananta matsalar.