The news is by your side.

Tattaunawar Iran da Amurka Na Fuskantar Barazana Saboda Rikicin Lebanon

53

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa Lebanon da sauran saɓani sun kawo cikas ga tattaunawar tsagaita wuta da Amurka.

Ya ce yarjejeniyar da ake dogaro da ita ta riga ta rushe, wanda ya sa ci gaba da tattaunawar ya zama mai wahala.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Ghalibaf ya ce Amurka ta saɓa yarjejeniya ta hanyar ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, kutsen jirage marasa matuƙi a Iran da kuma hana ƙasar haƙƙinta na tace sinadarin uranium.

Ya ce wannan hali na ƙara dagula dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan na zuwa ne yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta shiga rana ta biyu, a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, ciki har da babban birnin ƙasar Beirut.

Hukumar kare lafiyar jama’a ta Lebanon ta ce mutane 254 sun mutu, yayin da sama da 1,100 suka jikkata.

Amurka da Iran duk sun yi iƙirarin samun nasara a yarjejeniyar, amma rikicin ya ƙara tsananta bayan hare-haren da Isra’ila ta kai.

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya goyi bayan matakin na Isra’ila.

A gefe guda, Iran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani idan hare-haren ba su tsaya ba, yayin da ake shirin gudanar da muhimmin taro a Pakistan domin kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya.

Ƙasashen Turai da dama sun buƙaci a gaggauta kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Paparoma Leo ya bayyana wannan lokaci a matsayin “lokacin yin babban fata.”