The news is by your side.

Iran da Amurka Sun Amince da Tsagaita Wuta na Makonni Biyu, Tattaunawa Za Ta Gudana a Islamabad

58

Ƙasar Iran ta amince da tsagaita wuta na makonni biyu da Amurka ta gabatar, tare da sanar da cewa za a fara tattaunawa a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan a ranar Juma’a.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai dakatar da kai hare-haren da ake kaiwa Iran na wucin gadi domin bai wa ɓangarorin damar cimma yarjejeniya.

Ya ce sharaɗin tsagaita wutar shi ne Iran ta buɗe mashigin ruwa na Hormuz gaba ɗaya.

Rahoton ya samo asali ne daga majiyoyi da dama ciki har da hukumomin gwamnatin Iran.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da matakin, yana mai cewa ƙasar za ta dakatar da kai hare-haren ramuwa idan aka daina kai mata hari.

“Idan hare-haren suka tsaya, rundunoninmu za su dakatar da matakan mayar da martani,” in ji shi a wani saƙo da ya wallafa.

Ya kuma bayyana cewa za a ba jiragen ruwa damar wucewa cikin tsaro tare da haɗin gwiwar sojojin Iran.

Shugaban ƙasar Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa tsagaita wutar ya fara aiki nan take.

Sai dai Iran ta jaddada cewa tana shiga tattaunawar ne ba tare da cikakkiyar yarda da Amurka ba, tana mai cewa akwai rashin amincewa tsakanin ɓangarorin biyu.

Shirin da Iran ta gabatar mai ƙudirai 10 ya haɗa da ɗage takunkumi, biyan diyya, da kuma ficewar sojojin Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya.

Har ila yau, an buƙaci a tabbatar da yarjejeniyar ta hanyar ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya.

Masana sun ce wannan mataki na iya rage tashin hankali a yankin, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale me yawa.

A gefe guda kuma, Isra’ila ta nuna goyon baya ga matakin na Trump, amma ta ce ba zai shafi ayyukanta na soja a Lebanon ba.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya riga ya janyo asarar rayuka da dama da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi a duniya.