The news is by your side.

Ƙasashen Duniya Sun Yi Maraba da Tsagaita Wuta Tsakanin Amurka da Iran

66

Ƙasashe da dama a duniya sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, wadda za ta kai ga tattaunawar zaman lafiya a Islamabad.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce yana goyon bayan matakin, amma ya jaddada cewa ba zai shafi hare-haren da yake kaiwa Lebanon ba.

Haka kuma, ƙasashen Iraƙi da Masar sun buƙaci ɓangarorin su mutunta yarjejeniyar domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Waɗannan rahotanni sun fito ne daga hukumomi da dama ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yaba da matakin, yana mai cewa ya zama dole a kare rayukan fararen hula.

Ƙasashen Japan, Indonesia da Malaysia ma sun bayyana goyon bayansu, suna masu kiran a guji duk wani mataki da zai sake tayar da rikicin.

Haka kuma, Australia da New Zealand sun bayyana cewa tsagaita wutar na iya taimakawa wajen daidaita tattalin arziƙin duniya.

Masana sun ce mashigin Hormuz na da muhimmanci wajen samar da mai a duniya, don haka bude shi zai rage matsin tattalin arziƙi.

Duk da haka, sun yi gargaɗin cewa, dole ne a ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniya ta dindindin.

Wannan mataki na zuwa ne bayan makonni na tashin hankali da suka girgiza yankin Gabas ta Tsakiya.