The news is by your side.

Harin Ƴan Bindiga a Kebbi: Gidaje Sun Ƙone, Mutane Sun Tsere

53

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai farmaki cikin dare a wasu ƙauyuka a Jihar Kebbi, lamarin da ya jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyi.

Harin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyukan Gebe, Kawara da Kalkami a ƙaramar hukumar Shanga.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyukan ne ɗauke da makamai, inda suka buɗe wuta tare da ƙona gidaje da dama, lamarin da ya tilasta mazauna yankin tserewa.

Majiyoyi sun ce ana kyautata zaton maharan sun fito ne daga dajin Wawa da ke Jihar Neja.

Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da harin, tana mai cewa an tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya.

Kakakin rundunar, Bashir Usman, ya ce, “An tura jami’an tsaro ciki har da sojoji da ƴan sa-kai domin kare rayuka da dukiyoyi.”

Ya kuma jajanta wa iyalan da abin ya shafa, yana mai cewa ana ci gaba da bincike domin kamo masu laifi.

Rahotanni sun nuna cewa, ƙauyen Kawara ya fi shan wahala, inda aka ƙona gidaje da dama.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken adadin waɗanda suka mutu ba, amma ana fargabar an samu mace-mace da raunuka da dama.

Wannan lamari ya ƙara nuna tsananin matsalar tsaro a yankunan kan iyaka tsakanin jihohin Kebbi da Neja.