The news is by your side.

Barazanar Rufe Babul-Mandeb: Tashin Hankali Ya Ƙara Ƙamari A Gabas Ta Tsakiya

48

Wani babban mai ba da shawara ga jagoran Iran ya yi barazanar cewa ƙawayen ƙasar za su iya rufe mashigin ruwan Babul-Mandeb, kamar yadda aka yi a Hormuz, kamar yanda Al Jazeera ta rawaito.

Ali Akbar Velayati ya bayyana cewa idan Amurka ta ci gaba da barazana, za a iya dakatar da zirga-zirgar makamashi ta duniya.

“Idan White House ta maimaita kura-kuranta, za ta ga yadda za a dakatar da harkokin kasuwanci cikin sauƙi,” in ji shi.

Mashigin Babul-Mandeb yana da muhimmanci sosai domin safarar mai da kayayyaki tsakanin Asiya da Turai.

Rahotanni sun nuna cewa, kashi 10 cikin 100 na kasuwancin duniya na wucewa ta wannan hanya.

Masana sun yi gargaɗin cewa rufe mashigin zai iya haifar da babbar matsalar tattalin arziƙi a duniya.

Wani masani, Elisabeth Kendall, ya ce hakan zai zama “mummunan yanayi” ga kasuwancin duniya.

Rahoton ya kuma nuna cewa ƙungiyar Houthi ta Yemen na da ikon dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari a rana ta 38.