The news is by your side.

Ban Tsorata Ba – Seun Okinbaloye Ya Maida Martani ga Minista Wike

61

Ɗan jaridar Channels TV, Seun Okinbaloye, ya bayyana cewa bai tsorata ba duk da kalaman barazana da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi masa.

Ya bayyana hakan ne yayin shirin siyasa na Sunday Politics.

Ya ce, “Ina so in bayyana ƙarara, ba na jin tsoro kuma ba zan taɓa bari a tsoratar da ni ba.”

Wannan ya biyo bayan kalaman da Wike ya yi na cewa zai harbe shi saboda ra’ayinsa kan siyasa.

Okinbaloye ya jaddada cewa aikin jarida aikin bayyana gaskiya ne kuma dole ne a yi shi ba tare da tsoro ba.

Ya kuma ce hukumomin tsaro sun ba shi tabbacin kariya.

Ya ƙara da cewa, Wike ya tuntuɓe shi domin bayyana cewa bai nufin cutar da shi ba.

Sai dai ya jaddada cewa, kalaman tashin hankali ba su dace a demokaraɗiyya ba.

Ya ce, “Demokaraɗiyya na cikin haɗari idan aka hana ƴan adawa magana.”

Haka kuma ya gode wa ƙungiyoyi da mutanen da suka goyi bayansa.