The news is by your side.

Iran Ta Sassauta Takunkumi a Mashigin Hormuz, Ta Bai wa Jiragen Iraƙi Ƴancin Wucewa

78

Iran ta sanar da cewa jiragen ruwan Iraƙi za su ci gaba da wucewa cikin ƴanci a mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanya ta safarar makamashi a duniya, a wani sabon mataki na sassauta tsauraran matakan da ta ɗauka.

A cewar rahoton Al Jazeera, hedikwatar rundunar Khatamil-Anbiya ta Iran ta ce, takunkumin zai shafi “ƙasashen maƙiya” ne kawai, tare da jaddada girmama ikon Iraƙi.

Sanarwar ta ce, “muna girmama cikakken ikon Iraƙi,” tare da yabawa gwagwarmayarta da Amurka.

Wannan na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake matsa lamba kan Iran da ta buɗe mashigin ko kuma ta fuskanci hari, yana mai gargaɗin cewa “dukkan bala’i zai sauƙa kan Iran cikin sa’o’i 48”.

Sai dai Iran ta mayar da martani tana kiran kalaman nasa da “marasa tushe kuma na rashin hankali”.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta taƙaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin, wanda ke ɗaukar kusan kashi ɗaya cikin biyar na makamashin duniya.

Duk da cewa ana ganin ɗan sauƙi a kwanakin nan, bayanan jiragen ruwa sun nuna cewa, zirga-zirgar ta ragu da sama da kashi 90 cikin 100.

Rahotanni sun nuna cewa, a makon da ya gabata jirage 53 ne suka wuce ta mashigin, mafi yawa kenan tun bayan fara rikicin.

Hakan ya jawo tashin farashin mai a duniya, inda ɗanyen mai nau’in Brent ya haura dala 109 kan kowace ganga.

Iraƙi, ɗaya daga manyan masu fitar da mai a duniya, ta fi fuskantar illa, inda samar da mai ya ragu daga ganga miliyan 4.3 zuwa miliyan 1.2 a rana, lamarin da ke barazana ga tattalin arziƙinta.