The news is by your side.

Harin Jirage Marasa Matuƙi na Iran Ya Lalata Muhimman Wuraren Kadarorin Amurka a Kuwait

62

Kadarorin Amurka da ke Kuwait sun shiga cikin sahun wuraren da hare-haren Iran suka shafa a ƴan kwanakin nan, inda aka kai manyan hare-hare ta sama da jiragen marasa matuƙi (drones).

A cewar Al Jazeera, hukumomin ƙasar sun ce, an kai hari kan cibiyoyin samar da wutar lantarki da ta tace ruwan sha guda biyu, wanda ya haifar da “mummunar ɓarna”.

Haka kuma, ma’aikatar kuɗi ta Kuwait ta ce an kai hari kan harabarta da ke babban birnin ƙasar, yayin da wata gobara ta tashi a cibiyar man fetur ta Shuwaikh bayan wani hari na drone.

Kamfanin man fetur na ƙasar ya tabbatar da faruwar gobarar da lalacewar wasu muhimman kayayyaki.

Wannan lamari ya ƙara tayar da hankali a yankin Gulf, musamman idan har Amurka da Isra’ila za su ƙara tsananta kai hare-hare kan Iran.

Ƙasashen ƙungiyar GCC sun ce duk da cewa suna da ƙarfin mayar da martani, sun zaɓi nuna haƙuri domin kaucewa ƙarin tashin hankali.

Rahotanni sun nuna cewa ƙasashen yankin na kashe kusan dala biliyan 115 a duk shekara wajen tsaro, amma har yanzu suna fifita tattaunawa da neman sasanci.

Sai dai wasu daga cikinsu sun gargaɗi cewa, idan hare-haren suka ci gaba, za su iya sauya wannan matsaya domin kare muradunsu.