The news is by your side.

BUK Ta Sanar da Rasuwar Matar Prof. Attahiru Jega, An Yi Jana’izarta a Abuja

52

Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da rasuwar Hajiya Hadiza Attahiru Jega, matar tsohon shugaban jami’ar kuma tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega.

A cikin sanarwar da jami’ar ta fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar Lahadi, ta bayyana alhininta kan wannan rashi mai girma.

Sanarwar ta ce, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un,” tana mai addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama.

An kuma sanar da cewa, an gudanar da sallar jana’izarta a Masallacin Ƙasa da ke Abuja bayan sallar Azahar ranar Lahadi 5 ga Afrilu, 2026.

Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya tabbatar da rasuwar a wata tattaunawa ta waya, yana mai cewa, “Allah ya gafarta mata kurakuranta”.

Rasuwar ta jawo ta’aziyya daga ɓangarori daban-daban, musamman a fannin ilimi da harkokin gwamnati.

Mutane da dama sun bayyana ta’aziyyarsu ga iyalanta, suna roƙon Allah ya ba su haƙuri da juriya.

Ana ci gaba da ambaton kyawawan halayenta da gudunmawar da ta bayar ga al’umma.