The news is by your side.

Atiku Ya Yi Alƙawarin Goyon Bayan Duk Wanda Ya Samu Tikitin ADC a 2027

62

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai goyi bayan duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a 2027.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da DW Hausa, a daidai lokacin da ake taƙaddama tsakanin jam’iyyar da INEC.

Atiku ya yi watsi da damuwar cewa matakin INEC na iya raunana jam’iyyar, yana mai cewa akwai wani ɓangare da ke tsoron ƙaruwar ADC.

Ya ce, “za mu goyi bayan duk wanda ya zama ɗan takara, kuma ma mu nawa ne? uku ko huɗu?”

Ya kuma jaddada muhimmancin bai wa matasa da mata dama a siyasa.

Lokacin da aka tambaye shi kan yiwuwar goyon bayan matashi, ya ce, “eh, me zai hana?”

Atiku ya nuna damuwa kan matsalolin tattalin arziƙi da tsaro, yana mai cewa jama’a sun gaji da halin da ake ciki.

Ya ƙara da cewa, rashin aikin yi da rashin ilimi na ƙara haddasa rashin tsaro, yana zargin gwamnati da rashin ɗaukar matakan da suka dace.