Jam’iyyun siyasa na adawa a Najeriya sun buƙaci Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta tsawaita wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwani zuwa ƙarshen watan Yulin 2026.
Buƙatar na ƙunshe ne cikin sanarwar da aka fitar a ranar Asabar bayan taron ƙoli na jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.
Jam’iyyun da suka haɗa da ADC ƙarƙashin David Mark, PDP ƙarƙashin Kabiru Tanimu-Turaki, da NNPP sun ce jadawalin da INEC ta fitar na nuna wariya a kansu.
A cikin sanarwar, sun ce “ƙa’idojin da INEC ta fitar na baya-bayan nan suna zama ƙalubale ga jam’iyyun adawa tare da ƙaƙaba musu sharuɗɗa da wa’adi.”
Sun buƙaci a tsawaita wa’adin daga ranar 30 ga Mayu, 2026 zuwa ƙarshen watan Yuli domin samar da daidaito a tsakanin jam’iyyu.
Jam’iyyun sun kuma zargi jam’iyyar APC da ƙoƙarin raunana demokaraɗiyya mai jam’iyyu da dama tare da kafa tsarin jam’iyya ɗaya.
Sun ce za su yi adawa da duk wani yunƙuri na tilasta Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takara guda a zaɓen 2027.
Bugu da ƙari, sun buƙaci a cire shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, bisa zargin nuna ɓangaranci ga jam’iyyar APC.
Sun ce ci gaba da rike mukaminsa na iya kawo cikas ga sahihancin zaben 2027 da kuma tayar da rikici a kasar.
Haka kuma sun buƙaci majalisar dokoki ta ƙasa ta sake duba dokar zaɓe ta 2026, suna mai cewa wasu tanade-tanade na iya raunana tsarin demokaraɗiyya.
Jam’iyyun sun kuma yi kira da a saki ƴan siyasa da ake tsare da su kan laifukan da ake iya bayar da belin su domin tabbatar da cikakkiyar damar shiga siyasa.