Ƴan sanda sun cafke ɓarawon dabbobi da masu safarar ƙwayoyi, sun ƙwato dabbobi da kayayyakin haram a Jigawa

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta sanar da nasarorin da ta samu wajen yaƙi da aikata laifuka, ciki har da cafke masu laifi da ƙwato dukiyoyi a sassa daban-daban na jihar.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar a ranar 25 ga Afrilu, 2026, ya ce an kama Lawan Muhammad mai shekaru 24 daga ƙauyen Zurkuɗa a garin Sundimina bisa zargin satar tumaki 24 da raguna 4.

Sanarwar ta ce an sace dabbobin ne daga ƙauyen Jonge a ƙaramar hukumar Torro ta Jihar Bauchi, inda aka kama wanda ake zargin a ranar 23 ga Afrilu da misalin ƙarfe 10 na safe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar VGN.

Rundunar ta ce an ƙwato dabbobin kuma ana ci gaba da bincike domin gano masu su da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Haka kuma, a ranar 20 ga Afrilu da misalin ƙarfe 8:07 na safe, ƴan sanda sun samu kiran gaggawa kan wasu da ake zargi suna lalata wayoyin lantarki a Unguwar Kaya da ke karamar hukumar Roni.

Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin sun tsere bayan ganin ƴan sanda, inda suka bar wayoyin da suka lalata, yayin da ake ci gaba da farautarsu.

A wani samame, rundunar ta kama mutane uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, ciki har da Obinna Kingsley mai shekaru 28 daga Alanjo a Guri, Usman Mani mai shekaru 35 daga Kiyawa/Samma, da Ali Yusuf mai shekaru 18 daga Gwaram.

An ƙwato sama da ƙwayoyi 4,000 da suka haɗa da wiwi, Tramadol, Exol, da sauran kayan maye tare da kuɗaɗen da ake zargin na haramtacciyar sana’a ne.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargin kafin gurfanar da su a kotu, tare da jaddada ƙudirinta na yaƙi da laifuka a faɗin jihar.

'Yan SandaJigawaLaifukaNajeriya
Comments (0)
Add Comment