Donald Trump ya tsallake rijiya da baya bayan an farmake shi a Washington DC

Shugaban Amurka Donald Trump ya tsallake rijiya da baya bayan da jami’an tsaro suka fitar da shi daga wajen wani taro a otel ɗin Washington Hilton da ke Washington DC a daren Asabar bayan wani mutum ɗauke da bindiga ya buɗe wuta.

Fadar White House ta ce Trump, matarsa Melania Trump, mataimakin shugaban ƙasa JD Vance da sauran mambobin majalisar ministoci ba su ji rauni ba bayan harbin.

Rahotanni sun ce an harbi wani jami’in Secret Service amma rigar kariya daga harsashi ta kare shi daga samun jikkata.

A cewar jami’an tsaro, an kama wanda ake zargi mai suna Cole Tomas Allen mai shekaru 31 daga jihar California, kuma ana zargin ya yi aikin ne shi kaɗai.

Taron na ƙungiyar ƴan jarida masu kula da fadar White House na daga cikin manyan al’adu na shekara, amma an katse shi bayan jin ƙarar harbe-harbe a wajen ɗakin taron.

Ɗan jaridar Al Jazeera Chris Sheridan ya rawaito cewa an ji ƙarar harbi sau da dama a cikin ɗakin, lamarin da ya jefa mahalarta cikin firgici.

Trump ya rubuta a shafinsa na Truth Social cewa an kama mai harbin, yana mai yabawa jami’an tsaro kan aikin da suka yi.

Ya ce, “ni da uwargidan shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da sauran jami’ai muna cikin ƙoshin lafiya,” tare da sanar da cewa za a sake shirya taron cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Babban lauyan gwamnatin Amurka mai riƙon ƙwarya, Todd Blanche ya ce ana ci gaba da bincike kuma ana sa ran gurfanar da wanda ake zargi nan ba da jimawa ba.

Wannan lamari na daga cikin hare-haren da aka taɓa ƙoƙarin kai wa Trump, ciki har da wani hari a Pennsylvania a watan Yulin 2024.

AmurkaTrumpUSA
Comments (0)
Add Comment