Ƙungiyar jiragen ruwa ta duniya ta buƙaci Amurka da Iran su saki ma’aikatan jiragen da aka kama da gaggawa

Wata babbar ƙungiyar harkokin jiragen ruwa ta duniya, International Chamber of Shipping, ta yi Allah wadai da kama jiragen kasuwanci da Amurka da Iran ke yi tare da kiran a saki ma’aikatansu cikin gaggawa.

Daraktan harkokin ruwa na ƙungiyar, John Stawpert, ya bayyana wa Al Jazeera cewa ya kamata ma’aikatan jiragen ruwa su gudanar da aikinsu “cikin ƴanci ba tare da tsangwama ba.”

Ya ce kama jiragen domin dalilai na siyasa ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da ke kare ƴancin zirga-zirga a teku.

A cewarsa, “waɗannan mutane suna jigilar kayayyaki ne kawai, don haka ba za a yarda da kama jirage domin nuna iko na siyasa ba.”

Stawpert ya ƙara da cewa, shirin Iran na karɓar kuɗin haraji a mashigin Hormuz ba shi da tushe a dokar ƙasa da ƙasa, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya zama abin koyi mai hatsari a sauran mashigai a duniya.

Ya kuma nuna damuwa kan matakin Shugaban Amurka Donald Trump na toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran, yana mai cewa hakan ya ƙara jefa kamfanonin sufuri cikin rashin tabbas.

Ma’aikatun tsaron Amurka da Iran sun sanar da kama jiragen kasuwanci bi-biyu a makon da ya gabata, yayin da rikici ke ci gaba a mashigin Hormuz.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce ta kama jirgin Majestic X mai alaƙa da Iran a tekun Indiya, bayan kama wani jirgi mai suna Tifani a baya.

A gefe guda, rundunar IRGC ta Iran ta ce ta kama jiragen MSC Francesca da Epaminondas bisa zargin aiki ba tare da izini ba da kuma canza tsarin zirga-zirga.

Hukumomin Philippines sun tabbatar da cewa ƴan ƙasar su 15 na cikin jiragen, yayin da Iran ta tabbatar musu cewa dukkan ma’aikatan na cikin ƙoshin lafiya.

Stawpert ya kuma nuna damuwa kan kimanin ma’aikatan jiragen ruwa 20,000 da suka maƙale a yankin Gulf sakamakon rufe mashigin, yana mai cewa halin da suke ciki na iya jefa su cikin damuwa bayan makonni bakwai.

Ya buƙaci Amurka da Iran su mutunta ƴancin zirga-zirga a teku tare da gaggauta dawo da zirga-zirga kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.

AmurkaHormuzIranIsra'ilaJirgin RuwaLebanonSyria
Comments (0)
Add Comment