Wasu fusatattun matasa sun ƙone mutane uku da ake zargi da hannu a kisan basaraken Kwallak, Ponzhi Kwallak, a ƙaramar hukumar Langtang North ta Jihar Plateau a yammacin ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce an kashe basaraken ne a daren ranar Alhamis bayan wasu ɓatagari sun kai masa hari a gidansa suka harbe shi tare da sace babur da wayarsa.
Majiyoyi daga al’ummar yankin sun shaida wa jaridar PUNCH a Jos cewa lamarin ya jefa yankin cikin alhini tare da ƙara tayar da hankali.
Mazauna yankin sun ce, an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Juma’a yayin da suke ƙoƙarin sayar da babur ɗin da aka sace, inda suka amsa laifinsu.
To sai dai kuma, ana kan hanyar miƙa su ga jami’an tsaro ne wasu fusatattun mutane suka tare su kusa da sakatariyar ƙaramar hukumar Langtang North suka ƙone su.
Wani mazaunin yankin, Moses Yakubu, ya ce an kai wa basaraken hari ne bayan an ba shi sabon babur kwanaki kaɗan kafin kisan.
Ya ce, “wasu mutane sun bi shi gidansa, suka harbe shi, suka sace wayarsa da babur ɗinsa suka tsere.”
Wani mazaunin yankin, Danladi Mark, ya bayyana lamarin a matsayin sakamakon takaicin rashin tsaro da jinkirin samun adalci.
Ya ce matakin da al’umma ta ɗauka na nuna rashin gamsuwa da yadda ake kare rayuka da dukiyoyinta.
Sai dai ya gargaɗi cewa, wannan lamari na nuna yadda rashin amincewa da tsarin shari’a ke iya haddasa ɗaukar doka a hannu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Plateau, Alabo Alfred, da PUNCH ta yi bai yi nasara ba domin ba a samu amsa kan kiraye-kirayen wayarsa ba.