Shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata David Mark, ya yi gargaɗi kan taɓarɓarewar tsaro da raguwar ƴancin demokaraɗiyya a Najeriya.
Mark ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, ƙarƙashin jagorancin gwamna Seyi Makinde.
Ya ce Najeriya na fuskantar babban ƙalubalen tsaro, yana mai nuni da ƙaruwar ta’addanci, fashi da makami da sace-sacen mutane a faɗin ƙasar.
A cewarsa, “a shekarar 2025 kaɗai, an samu mutuwar sama da mutane 12,000 sakamakon rikice-rikice, wanda ya fi na wasu ƙasashen da ke cikin yaƙi.”
Ya ƙara da cewa aƙalla mutane 15 na mutuwa a kullum yayin da kusan 19 ake sacewa, tare da kimanin mutane 1,400 da aka kashe ko aka sace cikin watanni uku na farkon wannan shekara.
Mark ya zargi gwamnatin APC da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyi, yana mai cewa gwamnati ta fi mayar da hankali kan siyasa fiye da gudanar da mulki.
Haka kuma ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa domin karkatar da ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya.
Ya ce “ginshiƙin demokaraɗiyya shi ne bai wa jama’a zaɓi, amma ana ƙoƙarin hana su wannan dama.”
Mark ya jaddada cewa babu wata jam’iyyar adawa guda ɗaya da za ta iya fuskantar abin da ya kira tsari mai ƙarfi, yana mai kira da a samar da haɗaka mai ƙarfi.
Ya buƙaci shugabannin adawa su fifita muradun ƙasa sama da son rai, yana mai cewa lokaci ya yi da za a haɗa kai domin ceto Najeriya.