Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Katsina ta Arewa a zaɓen 2027.
Sirika ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke Katsina, yana mai cewa magoya bayansa ne suka buƙaci ya shiga takarar.
Ya ce idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.
Sirika ya taɓa zama dan majalisar wakilai tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007, sannan aka zaɓe shi Sanata a shekarar 2011.
A shekarar 2023, ma’aikatar sufurin jiragen sama ƙarƙashinsa ta ƙaddamar da kamfanin jiragen sama na Nigeria Air kwanaki uku kafin ƙarshen mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Wannan mataki ya janyo muhawara a faɗin kasar kan tsarin mallakar kamfanin, inda kamfanin Ethiopian Airlines ke da kaso 49 cikin 100, gwamnati ke da kashi 5, yayin da wasu ƴan kasuwa uku na Najeriya ke riƙe da kashi 46.
A halin yanzu, Hukumar EFCC na tuhumar Sirika da zargin cin zarafin muƙami da kuma bai wa ƴan uwansa kwangiloli na biliyoyin nairori lokacin da yake minista.