Trump Ya Tsawaita Tsagaita Wuta da Iran Yayin da Amurka Ke Jiran Sabuwar Matsaya daga Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci sojojin ƙasarsa su tsawaita tsagaita wuta da Iran tare da ci gaba da toshe tashoshin ruwan kasar, yana jiran shugabannin Tehran su gabatar da matsaya guda kan tattaunawa.

Trump ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a dandalin Truth Social, inda ya ce gwamnatin Iran na cikin rikice-rikice da ke hana ta gabatar da tsari mai ma’ana.

Ya ce matakin ya biyo bayan roƙon Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da Babban Hafsan Sojojin kasar, Field Marshal Asim Munir, suka yi masa na dakatar da duk wani harin soja kan Iran.

A cewarsa, “mun amince mu dakatar da harin har sai shugabannin Iran sun gabatar da tsari guda, kuma na umurci sojoji su ci gaba da toshe tashoshin ruwan Iran tare da kasancewa cikin shiri.”

Trump ya ƙara da cewa tsagaita wutar za ta ci gaba har sai an gabatar da wannan tsari kuma an kammala tattaunawa.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin Amurka da Iran ya ƙaru a farkon watan nan kan ikon mashigar ruwa ta Hormuz.

Mashigar na da matuƙar muhimmanci ga jigilar man fetur a duniya, lamarin da ke ƙara damuwa ga kasuwannin duniya.

Rahotanni sun nuna cewa Pakistan na taka muhimmiyar rawa a bayan fage wajen sasanta tsakanin Washington da Tehran.

Sai dai babu wani lokaci da aka ayyana da Iran za ta gabatar da tsarinta ko kuma lokacin da tattaunawar za ta kammala.

AmurkaHormuzIranTrump
Comments (0)
Add Comment