Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana a wata hira da aka watsa a shirin Soni Irabor Live na tashar News Central cewa Najeriya ba ta samu nasara a Yaƙin Basasa na 1967 zuwa 1970 ba sai da taimakon Jamhuriyar Nijar.
Ya bayyana cewa a lokacin yaƙin da ya fara ranar 6 ga Yuli, 1967 zuwa 15 ga Janairu, 1970, ana shigo da kayan tallafi ga sojojin Najeriya ta hanyar Nijar.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake sukar yadda gwamnatin Najeriya ta tafiyar da dangantaka da Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga Yuli, 2023 wanda ya kifar da Mohamed Bazoum.
Ya kuma soki yanke wutar lantarki da Najeriya ta yi wa Nijar, yana mai cewa hakan bai dace ba duba da rawar da ƙasar ta taka wajen gina madatsar ruwa ta Kainji.
A cewarsa, Najeriya ta rasa tasiri a nahiyar Afirka idan aka kwatanta da yadda take taka rawa a baya.
Ya tuna yadda Najeriya ta taimaka wa Angola da kuɗi kimanin dala miliyan 20 a shekarun 1970 wajen fafutukar neman ƴancin kai.
“Yau Najeriya ba ta kan teburin yanke shawara, me take tasiri a kai?” in ji Obasanjo.
Ya kuma zargi yadda aka tafiyar da ƙungiyar ECOWAS, yana mai cewa an lalata ta cikin gaggawa duk da shekaru 50 na gina ta.
Obasanjo ya yi mulkin soja daga 1976 zuwa 1979 sannan ya zama shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007.