Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ba da shawarar a ƙwato kuɗaden jama’a da aka yi amfani da su ba bisa ƙa’ida ba daga matakin gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi 27 tsakanin shekarun 2019 zuwa 2024.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an cimma wannan matsaya ne bayan gabatar da rahoton kwamitin kula da asusun gwamnati a zaman majalisa da aka gudanar a Dutse a ranar Talata.
Shugaban kwamitin, Sani Isyaku-Abubakar, ne ya gabatar da rahoton mai taken taƙaitaccen bayani kan binciken asusun gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi.
Ya ce kwamitin ya gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a da kuma cikakken bincike kan asusun da aka bincika daga 2019 zuwa 2024.
A cewarsa, an duba rahotannin ofishin babban mai binciken kuɗaɗe na jiha da na ƙananan hukumomi tare da takardun kuɗi da kwangiloli na ma’aikatu da hukumomi.
Ya ƙara da cewa an gayyaci kwamishinoni, sakatarorin dindindin da sauran jami’ai domin amsa tambayoyin da suka taso daga binciken.
Kwamitin ya gano wasu matsaloli kamar kashe kuɗaɗe fiye da kasafin da aka amince da shi da kuma raunin tsarin saye da sayarwa da tattara kuɗaɗen shiga.
Haka kuma, ya ce an samu biyan kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, takardun kuɗi da ba a iya tabbatar da su ba da kuma gazawar kiyaye bayanai a wasu ƙananan hukumomin.
Isyaku-Abubakar ya ce “kwamitin ya ba da shawarar a ƙwato kuɗaɗen da aka yi kuskure tare da ɗaukar matakan ladabtarwa ga jami’an da abin ya shafa.”
Ya kuma nuna cewa akwai matsalolin tsari kamar rashin ƙwarewa ga ma’aikatan kuɗi da kuma raunin bin dokokin kuɗi a jihar.
Shugaban majalisar, Haruna Aliyu, ya yaba wa kwamitin tare da tabbatar da cewa za a miƙa rahoton ga ɓangaren zartarwa domin ɗaukar mataki.
Majalisar ta amince da rahoton baki ɗaya bayan kaɗa ƙuri’a a zaman na ranar Talata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da saɓani ke ci gaba da bayyana tasakanin tsohon gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar wanda yai wa’adinsa na biyu a tsakanin 2019 zuwa 2023 da gwamna mai ci, Malam Umar Namadi.
A ƴan kwanakin nan dai an ga wasu jiga-jigan siyasa a jihar da ke da alaƙa ta kusa da tsohon gwamnan na ficewa daga APC zuwa ADC.