Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna bayan murabus ɗin da Comrade Abdulsalam Gwarzo ya yi.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, wanda ya ce an gabatar da sunan Garo ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.
Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus ne bayan rikici tsakaninsa da gwamnan sakamakon sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Rahotanni sun ce majalisar dokokin jihar ta fara shirye-shiryen tsige shi kafin ya miƙa takardar murabus ɗinsa.
Daga bisani, Gwarzo ya fice daga NNPP sannan ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Mustapha Muhammad ya ce naɗin Garo ya dace da tanadin sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka gyara.
Ya ce gwamnan ya yi tuntuɓa da masu ruwa da tsaki kafin gabatar da sunan Garo domin cike gurbin da aka samu.
A cewarsa, Murtala Sule Garo mai shekaru 48 gogaggen ɗan siyasa ne da ya shafe fiye da shekaru 20 yana riƙe muƙamai daban-daban.
Ya taɓa zama sakataren tsare-tsare na jam’iyya a jihar da kuma mai ba da shawara ga gwamna, sannan ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Kabo.
Haka kuma ya taɓa zama shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON) a Kano da kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu.
Gwamnatin ta ce naɗin nasa na daga cikin matakan inganta shugabanci da ci gaba da samar da ayyuka masu inganci a jihar.