Sabbin Hare-hare a Filato Sun Hallaka Mutane 6, Rashin Tsaro Ya Ƙara Ta’azzara

Aƙalla mutane shida ne suka rasu yayin wasu hare-hare guda biyu da aka kai a ƙananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi da ke Jihar Filato a Najeriya.

Hare-haren sun faru ne a ƙauyen Shonun da ke Riyom da kuma Hurum a yankin Gashish na Barkin Ladi a dare guda, a cewar Rahoton Ƙungiyar Matasan Berom (BYMA).

Mai magana da yawun ƙungiyar, Tengong Rwang, ya shaida wa Channels Television cewa maharan sun shiga ƙauyukan da manyan makamai a ƙafa.

Ya ce mutum huɗu ne suka mutu a Hurum yayin da wasu biyar suka samu raunuka, yayin da a Shonun kuma mutum biyu suka rasu wasu uku kuma ke asibiti.

Rwang ya ce mazauna Shonun sun riga sun sanar da jami’an tsaro kan shigowar wasu makiyaya da ba a san ko su waye ba kafin faruwar harin.

Ya ƙara da cewa al’umma sun riga sun fitar da mata da yara daga yankin saboda fargabar tashin hankali.

Ya kuma ce duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, har yanzu ba a samu isasshiyar kariya daga irin waɗannan hare-hare ba.

Rwang ya ce ƴan sa-kai sun yi ƙoƙarin kare al’umma amma an rinjaye su saboda ƙarfin makaman maharan.

Mai magana da yawun ƴan sanda a Filato, Alfred Alabo, ya ce ba a kai masa cikakken rahoto ba har zuwa lokacin da ake fitar da labarin, amma zai bincika ya bayar da bayani daga baya.

JosPlateauTsaro
Comments (0)
Add Comment