Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce gargaɗin da Hukumar Kula da Kafofin Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta fitar wani yunƙuri ne na tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar.
A jiya Asabar, NBC ta gargaɗi masu gabatar da shirye-shirye da su guji cusa ra’ayinsu a matsayin na gaskiya ko tsoratar da abokan tattaunawa a shirye-shiryensu.
Hukumar ta kuma ce, yayin da ƙasar ke shiga lokacin siyasa mai muhimmanci, dole ne a guji yaɗa labaran ƙarya.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren jiya Asabar, Atiku Abubakar ya ce wannan ƙa’ida wata hanya ce ta ƙoƙarin toshe bakin ƴan jarida.
Ya ce masana’antar yaɗa labarai ta Najeriya ta zama abin koyi a duniya, kuma abin damuwa ne yanda ake kawo irin waɗannan matakai lokacin da ake tunkarar zaɓe.
“Ina tare da kafafen yaɗa labarai da ke adawa da wannan yunƙuri na takura musu,” in ji Atiku Abubakar.
Ya ƙara da cewa, bai kamata a riƙa amfani da ƙa’idojin aikin jarida a matsayin makami a lokacin yaƙin neman zaɓe ba.
Atiku ya zargi gwamnati da mayar da hankali wajen neman ikon sarrafa labarai maimakon tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya.
Jam’iyyar APC na shirin tsayar da Bola Tinubu takara karo na biyu, yayin da jam’iyyun adawa suka haɗa kai ƙarƙashin jam’iyyar ADC.