Jami’an Rundunar Ƴan Sandan Jihar Ogun sun kama wani mutum mai suna Idowu Ashafa mai shekaru 43 bisa zargin mallakar sassan jikin ɗan Adam ba bisa ƙa’ida ba da kuma hannu a ayyukan tsafi a yankin Igbesa na jihar Ogun a ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026.
Kakakin rundunar, Oluseyi Babaseyi, ya bayyana cewa an kama mutumin ne da sanyin safiyar ranar yayin sintiri na yau da kullum da jami’an ƴan sanda ke gudanarwa.
A cewarsa, jami’an da ke karkashin jagorancin jami’in ƴan sanda na yankin, Solotan K. Owolabi, sun tare wanda ake zargin ɗauke da jakar leda da aka ɓoye sassan jikin ɗan Adam a ciki.
Ya ƙara da cewa an samu sabon kan mutum guda, tafukan hannu biyu, da sauran sassan jiki a cikin jakar da ake zargin ya ɗauka.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya tono waɗannan sassa ne daga wani kabari da ke ƙauyen Ido Itekun a yankin Igbesa domin amfani da su wajen ayyukan tsafi.
Babaseyi ya ce jami’an sun kuma ƙwato kayan aikin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata wannan laifi, tare da kai ziyara wurin da lamarin ya faru domin tattara bayanai.
Ya ce, “An kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar ranar 17 ga Afrilu, 2026, yayin sintiri, inda aka same shi da sabon kan mutum, tafukan hannu biyu da sauran sassan jiki a cikin jakar leda.”
A cewarsa, an mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan laifi a faɗin Jihar Ogun.
Kazalika, ya buƙaci mazauna yankin da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ƴan sanda mafi kusa domin taimakawa yaƙi da laifuka.