Iran ta gabatar da shirin buɗe Hormuz yayin da take jinkirta tattaunawa kan nukiliyarta da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya gabatar da wani sabon shiri na diflomasiyya domin buɗe mashigar ruwa ta Hormuz yayin da ya jinkirta tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliya, a wata ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan, Oman da Rasha.

A ranar Litinin, Araghchi ya gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin St Petersburg, bayan ya ziyarci Islamabad sau biyu inda ya gana da Firaminista Shehbaz Sharif, Ishaq Dar da Asim Munir.

Rahoton Al Jazeera ya ce an gudanar da muhimman tattaunawa a Muscat, Oman, kan tsaro da makomar rikicin, inda aka ware batun nukiliya zuwa gaba.

Iran ta gabatar da sabon shirin ta ga Pakistan domin kai saƙo tsakanin Tehran da Washington bayan tattaunawar ranar 11 ga Afrilu ta gaza.

Mai magana da yawun White House Olivia Wales ta ce Amurka ba za ta yi tattaunawa ta kafafen yaɗa labarai ba, kuma ba za ta amince Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa Fox News cewa Iran ta san abin da ake buƙata, yana mai cewa “ba za a bari su mallaki makamin nukiliya ba”.

A ƙarƙashin dokar War Powers Resolution ta 1973, Trump na da wa’adin ranar 1 ga Mayu domin neman amincewar Majalisa kan ci gaba da yaƙin.

Araghchi ya kuma tattauna da ministocin harkokin wajen Qatar, Saudi Arabia, Masar da Faransa ta wayar tarho.

Masana kamar Dania Thafer sun ce wannan yunƙuri na Iran yana nuna ƙoƙarin samun goyon bayan yankin kafin cimma yarjejeniya.

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko Amurka za ta amince da shirin.

AmurkaGabas ta TsakiyaHormuzIran
Comments (0)
Add Comment