Hukumar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) ta sanar da fitar da sakamakon dalibai 632,788 da suka rubuta jarrabawar UTME ta 2026 a ranar Alhamis 16 ga Afrilu 2026.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a.
Ya ce yanzu ɗalibai za su iya duba sakamakonsu ta hanyar aika saƙon “UTMERESULT” zuwa lambobin 55019 ko 66019 da layin da suka yi rajista da shi.
Hukumar ta bayyana cewa a halin yanzu ana iya duba sakamakon ne kawai, domin har yanzu ba a fara bayar da damar fitar da takardun sakamakon ba.
Ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da jarrabawar, kuma za a ci gaba da fitar da sakamakon sauran ɗaliban a hankali.
JAMB ta gargaɗi ɗalibai da su guji duk wani yunƙuri na sauyawa ko ƙirƙirar sakamakon jarrabawar.
Sanarwar ta ce irin wannan aiki laifi ne mai tsanani da zai iya jawo hukunci.
Ta bayyana cewa an riga an kama ɗalibai biyu da wani uba guda da ake zargi da yin maguɗin sakamako ta hanyar amfani da fasahar zamani.
A cewar Fabian Benjamin, “Mutanen uku na hannun hukuma saboda zargin yin maguɗin sakamako ta amfani da fasahar AI da sauran hanyoyin lantarki.”
Hukumar ta jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ta kuma buƙaci ɗalibai su bi hanyoyin hukuma kawai tare da kiyaye gaskiya yayin aiwatar da jarrabawar.