Farashin mai ya faɗi a duniya bayan Iran ta buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ragu a ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026 bayan Iran ta sanar da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci.

Farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya sauƙa zuwa dala 88 daga sama da dala 98 da ya kai a farkon ranar, a cewar rahotannin kasuwanni.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa “an buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya ga dukkan jiragen kasuwanci a lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke aiki,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa.

Mashigin Hormuz wata muhimmiyar hanya ce ta ruwa da ke haɗa Tekun Fasha da Tekun Arabia, inda kusan kashi ɗaya bisa biyar na man duniya ke wucewa.

Rahotanni sun nuna cewa kasuwannin hannayen jari na duniya sun farfaɗo bayan sanarwar, inda manyan kasuwannin Amurka suka samu ƙarin daraja.

A cewar bayanai, S&P 500 ya ƙaru da kashi 0.8 cikin ɗari, yayin da Nasdaq da Dow Jones suka haura kashi 1 cikin ɗari.

Haka kuma kasuwannin Turai sun tashi, inda CAC na Paris da DAX na Frankfurt suka ƙaru da fiye da kashi 2 cikin ɗari.

An rufe mashigin ne tun bayan hare-haren soji da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a Iran a ƙarshen watan Fabrairu, lamarin da ya jawo tashin farashin mai.

Rufe mashigin ya rage yawan mai da iskar gas a kasuwa, tare da haifar da hauhawar farashin man fetur da dizal.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi maraba da matakin Iran, inda ya rubuta a shafinsa na Truth Social cewa “mashigin ya buɗe gaba ɗaya.”

Sai dai daga bisani ya ce har yanzu ana ci gaba da ƙaƙaba takunkumin sojin ruwa ga Iran har sai an cimma yarjejeniya ta dindindin.

Danyen MaiFarashiHormuz
Comments (0)
Add Comment