Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki 10 tsakanin Isra’ila da Lebanon

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki 10 tsakanin Isra’ila da Lebanon bayan tattaunawa da shugabannin ƙasashen biyu.

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social, inda ya ce Shugaban Lebanon Joseph Aoun da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun amince da yarjejeniyar.

Ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawa kai tsaye tsakanin shugabannin ƙasashen biyu da aka gudanar a Washington ranar Talata, wadda ita ce ta farko cikin shekaru 34.

A cewarsa, tsagaita wutar za ta fara aiki da ne ƙarfe 5 na yamma agogon gabashin Amurka.

Trump ya ce, “Na yi tattaunawa mai kyau da Shugaba Joseph Aoun na Lebanon da Firaminista Bibi Netanyahu na Isra’ila, kuma sun amince da fara tsagaita wuta na kwanaki 10 domin samar da zaman lafiya.”

Ya ƙara da cewa ya umarci mataimakinsa JD Vance da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio tare da shugaban hafsoshin soji su haɗa kai da ɓangarorin biyu domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A baya dai rahotanni sun nuna cewa, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon duk da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla tsakanin Amurka da Iran.

Ofishin Netanyahu ya taɓa bayyana cewa yarjejeniyar bata shafar Lebanon, lamarin da ya sa hare-haren suka ci gaba.

Trump ya kuma ɗauki alhakin cimma yarjejeniyar, yana mai cewa wannan zai zama yaƙi na goma da ya taimaka wajen kawo ƙarshensa tun bayan dawowarsa kan mulki.

AmurkaIsra'ilaLebanonTrump
Comments (0)
Add Comment