Ƴan bindiga sun sace fasinjoji 14 ciki har da ɗalibai masu shirin rubuta JAMB

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla fasinjoji 14, ciki har da ɗaliban da za su rubuta jarabawar JAMB, a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo a Jihar Benue.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da daren Laraba yayin da fasinjojin ke tafiya cikin motar Benue Links daga Makurdi zuwa Otukpo.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce motar na ɗauke da kusan mutane 18 lokacin da aka tare ta da misalin ƙarfe 8 na dare kusa da Otukpo.

Majiyar ta ce mafi yawan waɗanda aka sace matasa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa rubuta jarabawar UTME da suka shirya yi ranar Alhamis.

Ta ce, “Mutane biyu ciki har da direban sun tsere, amma sauran fasinjojin an kai su cikin daji.”

Kwamishinan ƴan sandan jihar Benue, Ifeanyi Emenari, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutane 14 aka sace yayin da mutum ɗaya ya tsira.

Ya ce, “Ina Otukpo yanzu tare da tawaga ta, muna cikin daji muna jagorantar aikin ceto,” tare da ƙarin bayanin cewa bincike na ci gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya ce jami’an tsaro sun bazu a yankin domin ceto waɗanda aka sace.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-hare a sassan jihar Benue, wanda ke ƙara janyo damuwa kan tsaron matafiya musamman ma ɗalibai.

BenueIlimiNajeriyaTsaro
Comments (0)
Add Comment