FIFA ta tabbatar Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta 2026 duk da rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya ce Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta 2026 duk da rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Infantino ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron tattalin arziƙi da kamfanin CNBC ya shirya.

Ya ce, “Iran za ta zo tabbas, muna fatan zuwa lokacin za a samu zaman lafiya wanda zai taimaka.”

Ya ƙara da cewa Iran ta cancanci shiga gasar kuma ƴan wasanta na son fafatawa a wasannin da aka shirya yi a Amurka a watan Yuni.

A baya dai an nuna damuwa kan yiwuwar halartar Iran sakamakon rikicin da ya ɓarke bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kanta a watan Fabrairu.

Iran ta taɓa yin barazanar ƙaurace wa gasar tare da neman a mayar da wasanninta daga Amurka zuwa Mexico, amma FIFA ta yi watsi da buƙatar.

Bayan makonni na hare-hare, an cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu, duk da cewa ana ci gaba da taƙaddama a yankin.

Infantino ya jaddada cewa ya kamata a raba wasanni da siyasa, yana mai cewa wasanni na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan jama’a.

An shirya fara gasar cin kofin duniya ta 2026, wadda za ta ƙunshi ƙasashe 48, a ranar 11 ga watan Yuni.

AmurkaFIFAIranWord Cup
Comments (0)
Add Comment